Hukumpmin kasar Iraq sunce an kashe kimanin mutum 20 a wasu hare haren bamabamai da aka gudanar a yau Litinin.
‘Yna sanda sunce bamabamai uku da aka dana a kananan motoci da kuma hare haren nakiyoyi a sasssa dabam dabam a kauyen Kirkuk sunyi sanadiyyar mutuwar mutum 12, suka kuma raunata wasu 35.
Can da fari kuma wani bom din ya tarwatse a wani masallacin ‘yan mazhabin Shi’a dake birnin Bagadaza, inda ‘yan sanda suka ce ya hallaka mutum biyar, ya kuma raunata 15. Hukumomi sun kuma ce an sami gawar wani mutum a wata unduwa dake kudancin bagadaza ta Mahaweel.
A wani labarin na dabam, binciken jin ra’ayin jama’a ya nuna cewa al’ummar Iraqi kullun sai kara yanke kauna suke yi da wata kyakkyawar makoma ga kasar tasu, bayan mamayar shekaru hudu da Amurka tayi jagoranci.
Kamar yadda wannan bincike ya nuna, kusan kashi 86 bisa dari na mutanen da aka tambaya, suna da tsoron cewa tashin hankalin da ake ciki a kasar, zai shafe su, ko danginsu a wani lokaci nan gaba.