Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tun Cikin Watan Yuli Tattalin Arzikin Amurka Ya Fara Karaya


Sabon rahoton da ya fito kan tasirin tattalin arzikin Amurka ya nuna cewar tun watan Yulin da ya gabat har zuwa watan Satumba tattalin arzikin na Amurka ya fara durƙushewa, da hakan ya nuna Amerkawa sun fara shiga fatara da talauci.

Rahoton da a yau Alhamis ma’aikatar cinikayyar Amurka ta fitar da shi yayi bayanin cewar kuɗin sayen abin masarufin da kowane ɗan Amurka ke samu domin ɓatarwa, da kuma farashin kayan masarufin da Amurka ke yi duk sun yi ƙasa da sulusin goma daga cikin ɗari. Hakan ya nuna babban koma baya idan an kwatanta da tasirin kaurin aljihun Amerkawa watanni uku kafin fara shiga talaucin.

Kazalika ma‘aikatar ƙwadagon Amurka ta badasanarwar cewa ana ci gaba da samun ƙarin Amerkawa maras aikin yi dake karɓar agajin sayen abinchi, har yawansu yanzu ya kusa kaiwa miliyan biyar.

XS
SM
MD
LG