Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Litinin 'Yan Zanga Zanga A Thailand Sun Hana Majalisar Dokoki Yin Zama Ta Musamman.


'Yan hamayya a Thailand sun yi kira ga Gwamnati da ta fara tattaunawa da masu zanga zanga,da nufin rage zaman dar dar,bayan wata gagarumar zanga zanga a harabar majalisa ta hana zaman hadin gwiwar Majalisa.Wakilin Muriyar Amurka Ron Corben a rahoto da aiko mana daga Bangkok,yace a gangamin,dubun dubatan mutane da suke nuna kyamar Gwamnati da suka fito an yi ta cikin lumana,bayan da 'Yansanda da Jami'an tsaro suka bari a yi.

Gangamin dubun dubatan masu zangazanga kyamar nuna kyama kan gwamnati ne suka gewaye Majalisar dokoki a Thai fadar kasar a yau litinin,wadda ya tilasta kakakin Majalisa ya fasa zaman hadin gwiwa tsakanin Majalisun domin zartasda muhimman dokoki

Zuwa can kusan tsakar rana kakakan gamayyar masu rajin Demokuradiyya ko PAD,cikin murnar hakarsu ta cimma ruwa zuwa gayawa magoya bayansu cewa Gwamnati ta kasa yin zama da ta shairya.An yanke wuta a ginin Majalisa. Kungiyar PAD tayi kawanya ga gininda gudanarda harkokin Mulki tun cikin watan Agusta,da nufin kifarda gwamnatin,wacce suke ikirarin 'yar barandar tsohon PM Thaksin Shinawatra ce.

Tun safiyar yau litinin,Yansanda suka kyale dubun dubatan masu zanga zanga su hallara a gaban Majalisar dokokin. Yadda aka gudnarda zanga-zangar ta yau cikin lumana,sabanin irinta da akayi cikin watan Oktoba ne inda jami'an tsaro suka bude wuta da hayaki mai sa hawaye har mutum biyu suka mutu, 400 kuma suka jikkata.

A wasu sassan birnin kuma har wayau litinin din nan,daruruwan masu zanga-zangar nuna kyamar Gwamnatin sun tare hanyar shiga hedkawatar 'Yansanda da wasu muhimman ma'aikatu.

Chris Baker,marubuci ne,kuma mai sharhi kan siyasar ThaiLand yace kodashike zanga-zangr anyita cikin lumana,duk da haka har yanzu babu tabbas domin duka sassan biyu masu adawa, da magoya bayan Gwamnati duka suna neman gwada karfi da yawan magoya bayan domin samun rinjaye daga al'uma.Yace dabarun PAD shine maida karfi kan wasu cibiyoyi da suke da fice.

Babu shakka wannan dabarace mai kyau,da kungiyar PAD ta dauka na auna zanga zangar kan wasu muhimman wurare cikin fadar kasar. Hakika,musamman da farko suka mamaye gidan Gwamnati yanzu kuma Majalisa. Yanzu an kaiga za-ge-dantse,na nuna yawan magoya bayan da zasu bazu kan tituna ko muhimman wuraren gwamnati.Daga karshe Allh kadai yasan sakamakon haka.

Wannan zanga zangar tazo bayan an kammala wata irinta ta nuna goyon baya ga gwamnati,nan ma dubun dubatan mutane suka fito suna kiran a dawoda tsohon Gwamnatin PM Thaksin Shinawatra.

Kungiyar PAD tace tana tsoron Gwamnatin tana neman yin muhimman gyara ga tsarin Mulki da zasu dakatarda bincike da kararraki dake gaban kotu kan Thaksin,iyalansa,da kuma magoya baya.

XS
SM
MD
LG