Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsagerun Niger Delta Sunyi Marhabun Da Sakin Asari Dokubo


Kotun ta saki Mujahid Dokubo Asari a jiya Alhamis, saboda tabarbarewar lafiyarsa.

Dokubao Asari yayi magana da manema labarai bayan an sako shi, inda yace zai ci gaba da fafutuka a madadin jama’ar yankin Niger delta, wadanda yace suna da ‘yancin zabawa kansu makomar da ta dace dasu.

Masu gabatar da kara dai sun gindaya wadansu ka’idoji kafin a saki Dokubo, wadanda suka hada da hana shi shiga duk wadansu harkokin siyasa.

Dokubo Asari shine shugaban Mayakan Sa Kai na Jama’ar Niger Delta, kuma an tsare shi ne saboda tuhumar cin amanar kasa da ake yi masa.

Kungiyarsa na daya daga cikin dimbin kungiyoyin dake fafutukar nemawa yankin Niger delta karin kaso daga arzikin man fetur da ake samu daga yankin.

Kungiyoyin tsagerun Niger Delta sunyi marhabun da sakin nasa, inda suka ce wannan wata alama ce ta kyakkyawan fata daga sabon shugaba Umar Musa ‘Yar Aduwa.

XS
SM
MD
LG