Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Thailand Jami'an Tsaro Zasu Yi Amfani Da Lalama.


Friministan ƙasar Thailand yace jami‘an tsaron Thailand zasu ci gaba da amfani da lalama da tattauna domin warware rikicin zanga-zangar da dubban ’yan ƙasar keyi har suka je suka mamaye manyan tashoshin jiragen saman ƙasar biyu.

A wata sanarwar da friminista Somchai ya bayar ta gidan Telbijin na Thailand yau Juma’a anji yana cewa jami‘an tsaro zasu riƙa taka tsantsan, tare da shirya tattaunawa da shugaban shirya zanga-zangar, sai dai yaƙi yace uffan game da korar da ya yiwa babban jami’in ’yan sandar Thailand kwana guda bayan ya baiwa ’yan sandan umarnin su gaggauta kawo ƙarshen zanga-zangar nuna ƙin jinin Gwamnatin da ake ci gaba da yi.

Anga tulin ’yan sandan kwantar da tarzoma sun haɗu a filayen jiragen saman ƙasar biyu ɗauke da makamai amma basu nemi tarwatsa masu zanga-zangar da jam’iyyar hamayya ta PAP suka shirya ba.

XS
SM
MD
LG