Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koma Bayan Tattalin Arziki Yana Ci Gaba Da Razana Masu Zuba Jari


Koma bayan da ake ci gaba da samu a tasirin tattalin arzikin ƙasa da ƙasa na ci gaba da cusa tsoro a zukatan masu zuba jari, hakan kuma ya janyo wata gagarumar zubar gado yau a kasuwannin hada-hadar hannayen jari.

Yau juma’a a kasuwar hannayen jarin masana’antu ta Dow Jones nan Amurka akwai alamun hannayen jarin sun yi ƙasa sosai kafin kammala cin kasuwar yau Kazalika kasuwannin NASDAQ daS&P duk sun tsorata sosai ba’a gudanar dawata hada-hadar cinikayya ta kirki ba, an kuma sami faɗuwar kashi biyar daga cikin ɗari zuwa tsakar rana.

Haka abin yake a kasuwannin Asiya inda aka sami faɗuwar ƙididdigar hanayen jari a kasuwannin Japan da Hon Kong. A kasuwar Birtaniya ma a Turai samma tilo an sami faɗuwar hannayen jari da rubu’in kashi daga cikin ɗari.

XS
SM
MD
LG