Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Uwargidan Morgan Tsvagirai Ta mutu A Hatsarin Mota


Jam'iyyar adawa ta Zimbabwe tace uwargidan Firayim Minista Morgan Tsvangirai ta rasa ranta, shi kuma Prime Ministan ya sami raunuka a wani hatsarin mota da ya rutsa da su.

Kakakin Jam'iyyar MDC yace motar da Morgan Tsvangirai tare da uwargidansa, Susan da mai kare lafiyarsu da direba suke ciki, tayi taho mu gama da wata babbar mota a yau Juma'a, a kan wani titi, dake kilomita hamsin, daga babban birnin kasar Harare. Ita dai matar a nan take ta mutu.

A wata hira da yayi da manema labarai, kakakin MDC Nelson Chamisa bai tabbatar da mutuwar Susan kai tsaye ba, amma dai yace hadarin yayi muni kwarai, ya kuma ce Mr. Tsvangirai ya sami raunuka.

Babu bayanin halin da sauran mutanen dake tare da shi a cikin motar suke ciki. Dukkansu dai an garzaya da su zuwa wani asibiti a birnin Harare.

Kafofin MDC sunce Mr. Tsvangirai yana kan hanyarsa ne ta zuwa wajen wani taron gangami da aka shiorya yi a gobe Asabar, a lokacin da suka gamu da hadarin.

A halin da ake ciki kuma, 'yan sanda sun kame alkalin da a shekaran jiya ya bayar da belin babban jami'in jam'iyyar hamayya, kuma wanda Prime Minista Tsvangirai ya so ya nada Minista.

Hukumomi sunce ana zargin Majistare Livingstone Chipadze da laifin wuce gona da iri, saboda ya kyale lauyan Roy Bennet ya shigar da takardar neman beli a ranar Laraba.

Ba a dai saki Bennet ba, kuma Kotun kolin Zimbabwe ta yi watsi da belin na Majistaren ya bayar, sannan tace a ci gaba da rike Bennet gidan wakafi har sai an sa ranarb tuhumar cin amanar kasa da ake masa.

XS
SM
MD
LG