Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

VOA Zata Bullo Da Sabon Shiri Na Addinin Musulunci


Muryar Amurka zata bullo da wani sabon shiri a kan addinin Musulunci, mai suna Islam In Action, ko kuma Musulunci kenan a Harshen Hausa, domin kyautata fahimtar yadda addinin yake.

Shugabar Sashen Africa Gwendolyn F. Dillard da Shugaban Sashen Hausa Sunday Dare sune suka baiyana hakan a lokacin da suke karbar bakuncin Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu sa’ad Abubakar III, lokacin da ya ziyarci Muryar Amurka, a ci gaba da ziyarar aikin da yake yi a Amurka.

Suka ce an kirkiro shirin ne domin cika burin dimbin masu sauraron sashen Hausa, wadanda ke da kishirwar shirye shirye irin wadannan, sannan kuma a kara fadakar da masu sauraron VOA kan kyawawan akidojin addinin Musulunci.

Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar yayi murna da jin wannan labari, ya kuma yi alkawarin bayar da dukkan gudunmawar da ake bukata wajen nasarar shirin.

A lokacin da yake hira da Ma’aikatan Sashen Hausa, Sarki sa’ad Abubakar yace ya zo Amurka ne domin ya halarci wadansu taruka kan matsayin addinin Musulunci a kan wadansu al’amuran ci gaban zamani, kamar Dimokradiyya.

Ya kuma yi bayanin yadda shi da sauran shugabannin addinai a Najeriya suke tuntubar juna domin tabbatar da hadin kai da fahimtar juna, tsakanin Musulmi da Kiristoci.

Cikin wadanda suka tarbi Sarkin har da Tshohin Shugaban Sashen Hausa, wanda yanzu yake jagorancin Sashen Dangantakar Shirye Shirye da saura kafofin yada labarai na duniya, Steve Lucas.

A mako mai shigowa sarkin zai halarci wani taron karawa juna ilmin da Cibiyar Nazarin Al’amuran Zaman Lafiya, wato Institute of Peace, ta shirya a kan dangantaka tsakanin mabiya addinai mabambanta a Najeriya.

XS
SM
MD
LG