Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Kunar Bakin Wake A Iraqi Ya Kashe Mutane Tara Ya Jikkata Wasu Dama.


Rundunar ’yan sandan Iraqi ta bada rahoton cewar wani harin ƙunar baƙin wake ya kashe mutane tara da jikkata mutane goma sha biyar a Masallachin ‘Yan shi’a dake kudancin binrin Bagadaza.

‘Yan sandan suka ce an kai harin ƙunar baƙin waken ne kwana guda bayan da majalisar dokokin Iraqi ta kaɗa ƙuri‘ar amincewa yarjejeniyar tsaron haɗin gwiwa da Amurka domin baiwa sojin Amurka damar ci gaba da zama a Iraqi har zuwa shekara ta 2011.

Ƙungiyoyin siyasar ’yan Sunnin Iraqi sun goyi bayan shirin yarjejeniyar bisa sharaɗin cewa gwamnatin ‘yan Shi’a zata amince da ayi ƙuri‘ar raba gardama a kan shirin yarjejeniyar, sai dai fitaccen jagoran ’yan Shi’a Moqtada al-Sadr yayi kiran da a fito ayi zanga-zangar lumana domin la’antar shirin yarjejeniyar.

Sanarwar da ya bayar daga ƙasar Iran dake maƙwabtaka da Iraqi, Malam al-Sadr ya godewa ’yan majalisar dokokin Iraqi da suka amince da ayi ƙuri‘ar raba gardama cikin watanni shida kan shirin yarjejeniyar.

XS
SM
MD
LG