Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Bom A Agadez Ya Kashe ‘Yan Sandan Nijar Hudu


Jami’ai suna zargin ‘yan tawayen Kungiyar buzaye mai da’awar Tabbatar da Adalci da laifin dasa bom din.

A farkon wannan sheakarar Kungiyar da aka fi sani da sunan MNJ, ta shiga idon duniya, lokacin da ta kaddamar da hari kan ma’aikatun gwamnati da na kamfanonin kasashen waje, a Arewacin Nijar.

An dai taba samun tawayen buzaye a shekarun 1990. Kungiyar ta MNJ ta zarghi Gwamnatin kasar da kin cika ka’idojin yarjejeniyar 1995, inda suka yi alkawarin baiwa buzaye kwarya-kwaryan ikon cin gashin kai.

Ko a watanni biyu da suka wuce ma, a kalla sojojin kurfau 11 ne suka mutu sakamakon irin wadannan hare hare.

XS
SM
MD
LG