Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Sojojin Ruwan Amurka Na Fuskantar Tuhumar Kisan Kai


Yau ake tuhumar wasu sojojin Amurka da laifin kisan gillar wadansu farar hular Iraqi su 24, a garin Haditha, a watan Nuwamban da ya wuce.

Masu bincike na bin diddigin zarge-zargen dake cewa Sojojin sun kashe farar hular ne bayan wani bom da aka dasa a gefen titi ya kashe abokin aikinsu guda daya. Wadanda aka kashe din sun hada har da mata da kananan yara.

Lauyoyi masu kare wadanda ake tuhuma sunce farar hular sun mutu ne sakamakon musayar wuta tsakanin sojojin da ‘yan bibdiga, da ya rutsa dasu.

Tun da fari dai jami’an sojin sunce farar hula 15 aka kashe sakamakon musayar wutar. A farkon shekarar nan Jaridar New York Times ta bada rahoton cewa a kalla sojojin ruwa biyar ne zasu fuskanci tuhumar da ta kama daga kisan tsautsayi cikin sakaci, da kisan gilla.

XS
SM
MD
LG