Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Gudun Hijirar Darfur Na Ci Gaba da Shan Azaba


Tawagar ta wadda ta hada wadansu Amurkawa masu zaman kansu, sunce ‘yan gudun hijirar na fama da wahalhalun da suka hada har da rashin wadataccen tsaro. Kwanan nan tawagar ta dawo daga Chadi, inda suka ga ‘yan gudun hijira cikin tsananin cuta, yunwa da kuma firgici.

Sun shaida wa manema labarai a birnin New York jiya Juma’a cewa ‘yan gudun hijirar suna fuskantar wani abi mai kama da yakin kare dangi.

Wata jarumar Fim a nan Amurka, Mia Farrow, wacce ke rike da mukamin Jakadiyar Majalisar Dinkin Duniya ta Musamman, ba zai yiwu ana ji ana gani, a kyale mutanen da suka tsere wa munanan hare hare a garuruwansu, su mutu a sansanonin da ya kamata ace sun ceci rayukansu ba.

Tawagar ta roki kasashen duniya suyi wani abu cikin gaggawa, wajen taimakawa wadannan ‘yan gudun hijira, wadanda suka ce suna fuskantar mutuwa cikin azaba, kuma sannu a hankali.

XS
SM
MD
LG