Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Gudun Hijirar Somaliya Sun Fara Komawa Gida


Kimanin kashi daya bisa hudu na yawan mutanen da suka gudu daga Mogadishu saboda fadan da ake gwabzawa tsakanin gwamnati da masu kishin Islama, sun koma gida ya zuwa yanzu.

Wani mai magana da yawun hukumar ya fada a yau Juma’a cewa har yanzu dai mutane suna cikin mawuyacin halin rayuwa a birnin na Mogadishu. Har yanzu babu ruwan sha ko wutar lantarki, gashi kuma tsabtar muhalli ta zama wata babbar matsala, saboda tarin shara da aka gaza kwashewa a unguwanni da dama.

Yace yawanci masu dawowar sunyi zango ne a unguwannin Waberi da Xamar, da Jab-bab da Madina, inda ba a taba samun tashe tashen hankula tsakanin Gwamnatin Rikon Kwarya da ‘Yan Gwagwarmaya ba. Saidai Jami’in na Hukumar Mai Kula Da ‘Yan Gudun Hijira yace mutanen dake zaune a sauran unguwanni sun kasa komawa gida saboda rashin wurin da zasu zauna.

Hukumar tace wakilan Majalisar Dinkin Duniya sun gana da jami’an gwamnati a ranar talatar da Talatar da ta gabata, domin tattauna hanyoyin kaiwa mabukata kayan agaji. Tace sun tattauna a kan wani gagarumin aikin tsugunar da kimanin mutane dubu 300 a Mogadishu.

XS
SM
MD
LG