Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Najeriya Na Alhinin Shekaru Talatin Da Uku Da Rasa Murtala


A yau Juma'a tsohon Shugaban Najeriya Marigayi Janar Murtala Mohammed yake cika shekaru 33 da rasuwa. An dai kashe shi ne a wani yunkurin juyin mulki, ranar Juma'a, 13 ga watan Fabrairun shekarar 1976.

'Yan Najeriya suna tuna marigayi Murtala Muhammad a matsayin mutum na farko da yayi yunkurin mayar da kasar bisa tafarkin dimokradiyya, bayan mulkin soja karkashin mulkin Janar Yakubu Gowon har na tsawon shekaru tara.

Yayi alkawarin gudanar da zabe cikin shekaru hudu, wanda magajinsa Olusegun Obasanjo ya cika a ranar daya ga watan Octoban shekarar 1979, amma bayan shekaru hudu sai aka sake gudanar da wani juyin mulkin, bayan nan kuma aka sake wani juyin mulkin da ya kafa dambar dawwamar da rashawa da cin hanci a zukatan shugabanni.

A shekarun baya dai, gwamnatoci sukan gudanar da hidimomin tunawa da marigayi Murtala Mohammed a sassan kasar, inda akan yi tarukan laccoci da shirye-shirye na musamman, amma yanzu babu mai tunawa da shi, daga Jami'ar Bayero dake kano, sai iyalin sa, sai kuma abokan arziki 'yan kadan.

Murtala shine kuma shugaban da ya fara aiwatar da tabbatacciyar manufar yaki da rashawa da cin hanci, wanda wadansu ke zargin shine sanadiyyar makarkashiyar kashe shi. Haka kuma gudanar da wata manufa ta yaki da rashin da'a, musamman a ma'aikatun gwamnati.

Babban abin da ake tunawa da marigayi Janar Murtala a nahiyar Afirka, shine jawabin da ya gabatar a wani taron Kungiyar Hada Kan Afirka ta OAU, wanda ya zaburar da shugabannin kan 'yanci da diyaucin kasashen Afirka. A sakamakon wannan jawabi ne Shugabannin Afirka a wancan lokaci, suka marawa Jam'iyyar MPLA ta marigayi Augustinho Neto baya, ta kayar da Jam'iyyar Jonas Savimbi ta UNITA a babban zaben Angola.

XS
SM
MD
LG