Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cimma Yarjejeniyar Daunin Iko A Somalia.


Masu shiga tsakani sunce Gwamnatin wucin gadi ta Somalia ta sanya hanu kan yarjejeniyar daunin iko da wani reshen masu kishin Islama dake da sassaucin ra'ayi.

A laraban nan ce aka cimma yarjejeniyar a zagaye na baya bayan nan, a shawarwari da Majalisar Dinkin Duniya ta dauki nauyin shiryawa a Dijibouti.

A karkashin shirin,an kara wa'adin Majalisar dokokin kasar ta wucin gadi na wasu shekaru biyu,san nan aka kara kujeru domin wakilai daga bangaren masu hamayya na gamayyar masu fafutukar sake 'yento Somalia. Reshen yana da sassaucin ra'ayi da ya palle daga masu zazzafar ra'ayi ciki harda al-shabab.

Masu lura da al'amuran siyasa sunce 'yarjejeniyar daunin ikon ba za ta kulla kome ba wajen dai-daita al'amura a Somalia,ganin gwamnatin ta wucin gadi ba ta da iko in ba a fadar kasar Mogadishu ba.

XS
SM
MD
LG