Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Takarar Shugabancin Amurka Sun Dau Zafi         


'Yan takarar Shugabancin Amurka, Barack Obama na Jam’iyyar Democrat da John McCain na Republican, suna shirye shiryen karshe na shiga muhawara ta biyu a yau Talata, a yayin da yakin neman zabensu ya shiga wani yanayi na yayata bayanan fallasa kan juna.

A jiya litinin, wajen wani jawabi da ya gabatar ga wani gangamin dalibai, a garin Albuquerque, jihar New Mexico, Sanata McCain ya zargi Barack Obama da karbar gudunmawar yakin neman zabe daga hannun kamfanin bada rancen gina gidaje na Fanie Mae and Freddie Mac, wanda ya ruguje. Yace Obama ya rufe idanunsa daga mawuyacin halin da kamfanin ya shiga.

Shi kuma Sanata Barack Obama ya fitar da wani fim dake bayanin hannun McCain a wata badakalar kudi ta shekarun 1980.

McCain dai yana cikin ‘yan Majalisa biyar, wadanda aka lakabawa suna Keating Five, wadanda suka hana jami’ai daukar mataki a kan Charles Keating, shugaban wani banki da ya ruguje a karshen shekarun 1980. Daga karshe an sami Keatin da laifin magudi.

Da alamu dai harkar tattalin arziki ita ce zata fi daukar hankalin muhawarar ta gobe, musamman ganin yadda tattalin arzikin Amurka ya shiga mawuyacin hali.

XS
SM
MD
LG