A
wajen muhawarar da aka gabatar a garin Nashville na jihar Tennessee, Sanata
John McCain ya dora alhakin mawuyacin halin da tattalin arzikin kasar ya shiga
kan hadama da rashin kulawar shugabannin a Washington, da cibiyar Kasuwanci ta
Wall Street. Yace yayi kyakkyawan tanadin warware wannan matsala, kamar ta
hanyar wadata kasar da makamashi, da sanya hannun gwamnati domin tallafawa
wadanda suka kasa biyan basussukansu.
Shi
kuwa Sanata Obama cewa yayi hakika Amurka tana cikin wani mummunan halin
tattalin arzikin kasa, da ba a taba ganin irinsa ba tun daga wani na tarihi da
aka taba yi a shekarun baya, wato The Great Depression. Yace babu abin da ya
kawo wadannan matsaloli irin munanan manufofin tattalin arzikin gwamnatin
George Bush.
Babu
dai abin da McCain yake fatan yi a halin yanzu, irin ya cike ratar da Obama ya
bashi a kuri'ar jin ra'ayin jama'a.
Sabuwar
kuri'ar baya-bayan nan, wacce jaridar Washington Post da gidan talbijin na ABC
suka gudanar, ta nuna cewa a Jihar Ohio wacce take da muhimmanci ga takarar
shugabancin kasa, Obama ne yake kan gaba, inda ya sami maki 51 bisa dari, shi
kuwa McCain yana da 45 bisa dari.
Kuri'ar
jin ra'ayin jama'a da CNN ma ta gudanar ta nuna cewa Obama yana da maki 53,
McCain yana da maki 45.
Saidai
wata kuri'ar jin ra'ayin jama'ar da kamfanin Dillancin Labaru na Reuters, da
Gidan Talbijin na C-Span da wani kamfanin dake gudanar da irin wannan kur'ar
jin ra'ayin jama'a na Zogby, sun nuna sakamakon da ratartsa ta gaza na sauran,
inda suka ce da maki uku kawai Obama ya dara McCain.