Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yar Aduwa Kalau Yake - Inji Adeniyi


Kakakin Fadar Shugaban Nageria, Segun Adeniyi, yace hutun da Shugaba Umar Musa 'Yar Aduwa ya fara a yau, bashi da nasaba da matsayin lafiyar sa.

Wannan ma shine dalilin da Shugaban ya yanke shawarar zamansa a gida Najeriya, domin ya musanta rahotannin kafofin yada labarai dake cewa zai je wata kasa a duba lafiyar sa.

Yanzu Shugaban zai gudanar da hutun nasa ne tsakanin gida Katsina da wuraren shakatawa na cikin gida.

Mataimakin Shugaba Goodluck Jonathan shine zai gudanar da harkokin kasa kafin Shugaban ya kammala hutun sa.

XS
SM
MD
LG