Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yar Aduwa Ya Lashe Zabe


‘Yar Aduwa yace bashi da wani abin yai sakamakon wannan nasara, illa godiya ga Allah, amma Janar Muhammadu Buhari baiyi wata-wata ba, yayi watsi da sakamakon zaben, har ma yace jam’iyyarsa zata gabatar da korafinta ga hukumomin da suka dace.

Wadansa suka sa ido kan yadda zaben ya gudana, na gida da na waje, sunce an tafka kura-kurai da yawa a zaben, cikinsu kuwa har da satar akwatunan zabe, tursasa masu kada kuri’a daga jami’an tsaro da kuma bude runfunan zabe a makare, koma aki buda su kwata-kwata.

Kasar Amurka ma ta bada sanarwar cewa rahotannin farko da take samu, sun nuna cewa akwai kura-kurai a zaben.

Ma’aikatar harkokin Wajen Amurka tace har yanzu jami’an gwamnatin Amurka suna tattara bayanai, suna kuma nazarinsu, da niyyar fito da wata tartibiyar matsaya a kan sakamakon.

Amma a yau Litinin, kakakin Ma’aikatar Harkokin wajen Amurkan, Sean McCormack ya bada sanarwar dake cewa hakika zaben yana cike da kura kurai, a wasu lokutan ma, manyan kura kurai.

XS
SM
MD
LG