Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ake Bude Wani Sabon Yunkurin Sulhu Da ‘Yan Tawayen Darfur


Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Taraiyar Africa zasu yi wani taro a kasar Tanzaniya, domin tattauna yadda za a shawo kan ‘yan tawayen Darfur su koma kan teburin tattauna sulhu.

Koda yake ana sa ran fara wannan taro na kwan uku a yau Juma’a, a birnin Arusha, ba a tantance wadanne kungiyoyin ‘yan tawaye ne zasu halarci taron ba.

A wani bayani ga Majalisar Dinkin Duniya jiya Alhamis, Jakadan Kwango, Pascal Gayama yace tattaunawar ta Tanzaniya zata maida hankali ne wajen matakan siyasa da za a dauka wajen dawo da zaman lafiya ga wannan yanki da ya sha fama da matsalar yaki.

A wani bangare na dabam, Kwamishinan Kungiyar Taraiyar Africa, mai kula da al’amuran zaman lafiya, Sa’id Djinnit yace kasashen Africa biyar, Burkina Faso, Kamaru, Najeriya, Masar, da Habasha sunyi alkawarin bayar da karonsu na sojoji ga rundunar da ake shirin kafawa ta Darfur.

Faransa ma tace zata tura nata dakarun.

XS
SM
MD
LG