Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Fashin Jirage A Somaliya Suna neman Diyyar Dala Milyan Biyu.


Jami’ai a Yemen sun ce masu fashin jirage daga Somalia suna neman a biyasu dala milyan biyu a matsayin kuɗin fansa kan jirgi na baya bayan nan da suka ƙwace a mashigin ruwan Aden.

Kamfanin dillancin labarai na Yemen ya laburta cewa jirgin Adina yana ɗauke ta ton ɗari biyar na baƙin ƙarfe a kan hanyarsa zuwa tsibirin Socotra lokacin da aka sace shi cikin wannan makon. Jami’an sun ce ma’aikatan jirgin sun haɗa da ’yan ƙasar Somalia guda uku da ’yan ƙasar Yemen biyu da kuma na Panama biyu.

Yanzu haka ’yan fashin jirgin suna garkuwa da jiragen ruwa goma sha biyar da suka haɗa da jirgin Saudiya dake ɗauke da mai da aka ƙiyasta kuɗinsa a kan dalar amurka miliyan ɗari. Yan fashin sun yi rangwami a kuɗin fansar da suka nema a kan jirgin daga dala miliyan 25 zuwa 15.

XS
SM
MD
LG