Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zimbabwe Ta Sami Tayin Tallafi Na Farko Daga Turai


Kasar Australia tace zata bada tallafin kudi ga gwamnatin hadin kan kasa ta Zimbabwe, al'amarin da yasa Australiyan ta zama kasar Turai ta farko da zata baiwa sabuwar gwamnatin ta Zimbabwe tallafi kai tsaye.

A Wata sanarwa da ya bayar a ga Majalisar Australiya a yau Laraba, Ministan harkokin Wajen kasar, Stephen Smith yace zasu baiwa Zimbabwe dollar miliyan goma, domin samar da ingantaccen ruwan sha, tsabtar muhalli da aiyukan lafiya.

Smith yace a 'yan shekarun baya, Australiya tana bayar da gudunmawar jin kai ne kawai, ta hannun kungiyoyin agaji, saboda tsoron da ake yi na cewa gwamnatin Shugaba Robert Mugabe zata iya sarrafa kudin ta wadansu hanyoyi.

A wani labarin kuma, a yau ake hidimomin binne uwargidan Prime Minista Morgan Tsvangirai, a gidansu na gado dake wani kauye a kudu da babban birnin kasar, Harare.

Tun jiya Dubban mutane, cikin su har da Shugaba Robert Mugabe ke ta halartar hidimomin jana'izar Susan Tsvangirai, domin karrama ta, bayan da ta rasu a wani hatsarin mota da ya rutsa da ita a ranar Juma'ar da ta gabata.

XS
SM
MD
LG