Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Mai Barin Gado GeorgeBush ,Zai Karbi Bakuncin Shugaban Amurka Mai Jiran Gado Barack Obama A Fadar White House.


A yau litinin ce shugaba Bush da uwargidansa Laura ke karɓar baƙuncin shugaba mai jiran gado Barack Obama tare da uwargidansa Michelle Obama a fadar shugaban Amurka ta White House. Wannan ne karon farko da sassan biyu zasu yi tozali da juna tun kammala zaɓen shugaban ƙasa a Talatar data gabata. Shugabannin biyu zasu tattauna ne ajandar tsara miƙa mulki daga hannun shugaba mai barin gado zuwa hannun shugaba mai jiran gado. A dai dai lokacin da shugabannin biyu ke tattaunawa, ita kuma uwargidan shugaba Bush ta ɗauki uwargida Michelle Obama domin zagayawa da ita loko-lokon fadar shugaban ƙasa ta White domin nuna mata dukkan lungunan gida da abubuwan da aka tanadarwa gidan. A halin da ake cikin shugaba Bush mai barin gado yace zai baiwa sabon shugaba Barack Obama mai jiran gado cikakken goyon baya a tattaunawarsu fuska da fuska.

XS
SM
MD
LG