WASHINGTON,DC —
A shirin A Bari Ya Huce na wannan makon daga cikin labaran da muka bayar akwai labarin saurayin da ya rika cika baki wai shi gagararre ne da kowa yake tsoro a gari, bayanda dan sanda ya tasa shi gaba yaje caji ofis ya maimaita abinda ya fada a mota, sai yace wallahi dama a unguwarsu duka sun san shi sarkin karya ne.
TAMBAYA: A ganinku ya kamata a sake shi ko kuma a tuhume shi da laifin da ya yi kurin cewa ya aikata?
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.