WASHINGTON, DC —
To a dai-dai wannan lokaci da aka fara gasar cin kofin duniya, a karonta na farko zuwa gasar, Bosnia bata da niyyar saka dan wasa daya kula da Messi na Argentina a koda yaushe a wasan da suke gabannin yi.
Bosnia ta samu nasarar zuwa gasar cin kofin duniya a karo na farko, bayan jefa kwallaye 30 a wasannin kwalifaya.
To amma manazarta sunce yin irin wannan wasa a wasansu na farko a gasar, da Argentina zai nuna karfin gwiwa, ko kuma rashin hikima. Amma kamar akwai take-taken cewa abunda kwach Safet Susic zai yi kennan.
Kwach Susic yayi suna wajen rike akidar kai hare-hare kawai, kuma ko da wa yake bugawa. Kuma da alama kamar ba zai canza yanda yake wasa ba, a arangamar da zaiyi da Argentina dake da Lionel Messi wanda yaci kyautar fitaccen dan wasan duniya sau 4.
Kwach din yace yana shakkar tanadin dan wasa wanda aikinsa kawai ya rike Messi. Yace baya tunanin akwai hikima a hakan. Mr. Susic yace bai taba amfani da ‘yan wasanshi ba wajen rike wani dan kwallo a ko da yaushe.