Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amanda Gorman Ta Sake Haskawa a Wasan Super Bowl


Lokacin da Amanda Gorman take wakar-baka a wajen bikini rantsar da Biden a ranar, 20 Janairu, 2021.
Lokacin da Amanda Gorman take wakar-baka a wajen bikini rantsar da Biden a ranar, 20 Janairu, 2021.

Matashiyar nan da ta ja hankalin Amurkawa da wakar-baka a bikin rantsar da shugaba Joe Biden a watan da ya gabata, ta sake haskawa a wasan karshe na gasar kwallon kafar Amurka wato Super Bowl.

Amanda Gorman, mai shekara 22 ta karanto wata wakar-baka a ranar Lahadi gabanin a fara wasan karshen a birnin Tampa da ke jihar Florida.

Wakar mai taken “Chorus of Captain,” wato “amshin jagororin wasa,” sadaukarwa ce ga wasu mutane uku kan irin rawar da suka taka a wannan lokaci na annobar Coronavirus.

Mutanen sun hada da mai karantarwa Trimaine Davis, mai aikin jinya Suzie Dorner da kuma tsohon soja James Martin.

Ita dai Gorman ta bayyana ne ta kafar wani bidiyo da aka nada, ba wai a filin wasa ta yi wakar ba, bidiyon da yake dauke da hotunan Davis, Dorner da Martin.

Ga kadan daga cikin baitukan wakar bakar:

“Mu yi tattaki da wadannan jarumai,

Mu zabura da wadannan zakaru,

Don mu mika sakon jagororinmu,

Muna jinjina masu a bayyane,

Da kwarin gwiwa da shauki,

Ta hanyar yin abin da ya kamata ta hanyar adalci

Yayin da muke karrama su a yau,

Su a kullum suke karrama mu.”

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG