Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutane Akalla 30 A Ghana


Wani mutumi yana ficewa daga gidansa da ruwa ya malale a unguwar Ashiaman a bayan garin Accra, litinin 21 Yuni 2010.

Hukumomin Ghana sun bayyana wannan ambaliya a Accra da tsakiyar Ghana a zaman mafi muni da aka gani cikin 'yan shekarun nan a kasar.

Adadin mutanen da suka mutu a sanadin ambaliyar ruwa a kasar Ghana ya karu zuwa akalla 30, daga adadin 23 da aka bayyana jiya litinin. Shugaban hukumar kula da ayyukan gaggawa a kasar Ghana, Kofi Portuphy, shi ne ya tabbatar da sabon adadin ga 'yan jarida talatar nan.

Wannan ambaliya ta fi yin barna a yankunan dake kewayen Accra, babban birnin kasar da kuma yankin tsakiyar Ghana.

Wannan ambaliya, wadda ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haddasa ta, ta kwashe motoci ta lalata gidaje, yayin da ta sa daruruwan mutane suka rasa wurin kwana.

Jami'an Ghana sun bayyana wannan ambaliya a zaman mafi muni da suka taba gani cikin 'yan shekarun nan.

Daminar dake kewayowa shekara-shekara a yankin Afirka ta Yamma ta kan haddasa ambaliyar ruwa. A shekarar 2009, ambaliya ta kashe mutane fiye da 100 ta kuma sa mutane miliyan biyu da rabi suka rasa matsuguni cikin kasashe 8 a yankin.

XS
SM
MD
LG