Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Jana'izar Marigayi Shugaba Umaru Musa 'Yar'aduwa


An binne marigayi shugaban Najeriya, Umaru Musa 'Yar'aduwa, a yayin da aka rantsar da Goodluck Jonathan a matsayin sabon shugaban kasa

An binne shugaba Umaru Musa 'Yar'aduwa na Najeriya a jiharsa ta Katsina, kasa da kwana guda a bayan rasuwarsa yana da shekaru 58 da haihuwa.

Dubban mutane sun cika filin wasa na Katsina alhamis domin sallar jana'izar marigayin, sannan suka raka gawarsa har zuwa makabarta inda aka binne shi. An nuna jana'izar ta sa kai tsaye a gidan telebijin na kasar.

Shugaban ya shafe fiye da watanni biyar yana kwance da rashin lafiya, kuma an san yayi fama da ciwon koda da kuma na kumburin rigar zuciya.

Tun fari alhamis da safe an rantsar da sabon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, a wurin wani bukin da aka yi a Abuja, babban birnin kasar.

Mr. Jonathan shi ne mataimakin shugaba 'Yar'aduwa kafin majalisar dokoki ta nada shi shugaban riko a watan Fabrairu a saboda jimawar da 'Yar'aduwa yayi yana fama da rashin lafiya.

A cikin wani dan gajeren jawabi da yayi, Mr. Jonathan ya yabawa 'Yar'aduwa a zaman amintacce mai rikon amana da gaskiya, ya kuma ce yayi jimami sosai da rasuwar shugaban.

Har ila yau, yayi alkawarin yaki da zarmiya da cin hanci, da gudanar da zabe na gaskiya, da kuma kokarin wanzar da zaman lafiya a yankin Niger Delta mai fama da fitina.

Marigayi Umaru Musa 'Yar'aduwa ya rasu laraba da maraice a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Shugabannin duniya da dama, ciki har da shugaba Barack Obama na Amurka, da Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, sun bayyana jimaminsu da rasuwar shugaba 'Yar'aduwa. Sun yaba ma 'yar'aduwa saboda kokarinsa na ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar Afirka, da kuma a cikin gida Najeriya a yankin Niger Delta, inda tsagera suka jima su na yakar kamfanonin mai.

XS
SM
MD
LG