Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar Da Wani Sabon Kamfen Yaki Da Cutar Shan Inna


Wata ma'aikaciya tana raba maganin rigakafin shan inna
Wata ma'aikaciya tana raba maganin rigakafin shan inna

An kaddamar da wani sabon tsarin yakin cutar shan inna. Cibiyar yaki da cutar shan inna ce ta kaddamar da sabon kamfen na tsawon shekaru shidda a Abu Dhabi.

An kaddamar da wani sabon tsarin yakin cutar shan inna. Cibiyar yaki da cutar shan inna ce ta kaddamar da sabon kamfen na tsawon shekaru shidda a Abu Dhabi. Wannan kamfen shine irinshi na farko da cibiyar ta kaddamar da nufin shawo kan dukan nau’in cutar shan inna. Idan aka sami tallafin kudin da ake bukata, za a yiwa sama da kananan yara miliyan dari rigakafi.

Cibiyar yaki da ciwon shan inna tace.wannan ne tsari na farko da aka kaddamar da nufin yaki da kowanne irin nau’in kwayar cutar shan inna. Jami’an kiwon lafiya sun bayyana cewa wadansu lokuta kwayar cutar da rigakafin da ake digawa a baki yake kwantarwa tana kin jin magani ta sa kananan yara su kamu da cutar shan inna daga baya, dalili ke nan da yasa aka gabatar da wannan sabon tsarin.

Idan aka sami kudin da ake bukata na aiwatar da wannan sabon shirin,, za a yiwa kimanin sama da kananan yara miliyan dubu dari rigakafi, wanda kuma bisa ga cewarsu zai zama matakin farko na shawo kan cutar. Kwararru suna kyautata zaton cimma nasara wajen kawar da cutar baki daya.

A halin yanzu dai kananan yara goma sha tara ne aka tabbatar suna dauke da kwayar cutar shan inna a duniya, adadin mafi kankanta da aka taba samu a tarihi.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG