Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya Ya Kafa Ma Iran Sabon Takunkumi


Taron Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya

Wakilai 12 daga cikin 15 na Kwamitin Sulhun majalisar sun yarda da kafa sabon takunkumi na hudu a kan kasar Iran saboda shirinta na nukiliya da ake gardama a kai.

Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya amince da sabon takunkumi kashi na hudu a kan kasar Iran a saboda shirinta na nukiliya da ake gardama a kai.

12 daga cikin wakilai 15 na Kwamitin Sulhun sun jefa kuri'ar yarda da kafa takunkumin yau laraba. Kasashen Brazil da Turkiyya sun jefa kuri'ar kin yarda, yayin da kasar Lebanon ta kaurace ma jefa kuri'a.

Kudurin takunkumin ya hada da tarnakin tafiye-tafiye da na kudi a kan wasu mutane da cibiyoyi masu alaka da shirye-shiryen nukiliya da na kera makamai masu linzami dake cin dogon zango na kasar Iran, ciki har da rundunar zaratan sojojin Iran mai suna Revolutionary Guard da kamfanin safarar jiragen ruwan jamhuriyar Islama ta Iran.

Har ila yau, takunkumin ya fadada takunkumin makaman da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa kan Iran a can baya, ya kuma hada da bangaren banki na kasar.

Jakadiyar Amurka a majalisar, Susan Rice, ta ce ba wai an kafa wannan takunkumin a kan al'ummar kasar Iran ba ne, an kafa shi ne a kan gurin mallakar nukiliya na gwamnatin da ta zabi hanyar maida kanta saniyar ware.

Amma jakadan Brazil a Majalisar Dinkin Duniya, ya ce kafa takunkumi ba hanya ce mai nagarta ta warware matsalar ba, kuma zata iya jefa al'ummar kasar Iran cikin wahala. Har ila yau ya ce takunkumin zai iya gurgunta yarjejeniyar da Brazil tana cikin wadanda suka shiga tsakani aka kulla, wadda a karkashinta Iran zata aike da wani bangare na karfen Uranium dinta zuwa Turkiyya domin a musanya mata da mai na nukiliya.

Shugaba Mahmoud Ahmadinejad yayi gargadin cewa kafa sabon takunkumi yana nufin karshen aniyar Iran ta tattaunawa da manyan kasashen duniya kan shirin nukiliyar kasar.

XS
SM
MD
LG