Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kawo Karshen Gangamin Masu Zanga-Zangar Kin Jinin Gwamnatin Thailand A Bangkok


Akalla hudu daga cikin shugabannin 'yan zanga-zangar sun mika kai ga 'yan sanda a bayan da suka bayyanawa magoya bayansu cewa zasu kawo karshen wannan gangami domin kawo karshen zub da jini

Shugabannin zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati a Thailand sun bayar da sanarwar kawo karshen wannan gangami na watanni biyu, a bayan da dakarun tsaron kasar suka dauki matakan babu sani ba sabo a kan tungar da 'yan hamayyar suka kafa a yankin kasuwanci na tsakiyar birnin.

Akalla hudu daga cikin shugabannin wadannan 'yan hamayya da ake kira Masu Jajayen Riguna sun mika kawunansu ga 'yan sandan Thailand, jim kadan a bayan da suka fadawa magoya bayansu cewa zasu kawo karshen wannan gangami domin hana ci gaba da zuba da jini.

Amma jim kadan a bayan da Masu Jajayen Rigunan suka ayyana kawo karshen wannan gangami, an ji karar fashe-fashen gurneti da dama a yankin, abinda ya raunata sojoji biyu da wani dan jarida dan kasar Canada.

An kashe mutane akalla hudu, wasu da dama suka ji rauni a lokacin da sojoji suka kutsa cikin sansanin Masu Jajayen Riguna yau laraba a inda wani filin shakatawa mai suna Lumpini Park yake, sa’o’i a bayan da suka yi amfani da motoci masu sulke domin farfasa shingayen da aka kakkafa a kewayen wannan sansani. ‘Yan zanga zangar masu jajayen riguna sun cunna wuta a jikin tayu da itatuwan gwangwala da suka kewaye wurin da su, abinda ya haddasa bakin hayaki da ya tashi ya turnuke sama daga wannan wuri.

XS
SM
MD
LG