Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Nada Sabon Jami'in Yaki Da Ta'adanci a Najeriya


Shugaban kasar Najeriya Goodluck JonathanNigeria
Shugaban kasar Najeriya Goodluck JonathanNigeria

Shugaba Goodluck Jonathan ya nada Manjo-Janar Sarki Bello ya maye gurbin Zakari Ibrahim a mukamin mai ba shi shawara a fannin yaki da ta'addanci

Makonni biyu kenan da shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya sallami mai bashi shawara a fannin yaki da ta’addanci bayan wani harin bom da ya halaka mutum 23 a kalla a helkwatar MDD a Abuja babban birnin tarayyar kasar.

A bayanin da ya yi a yau alhamis, kakakin fadar shugaban kasar Najeriya Reuben Abati bai fayyace dalilan sallamar Zakari Ibrahim daga mukamin shi ba. Amma dai kakakin ya ce an nada Manjo-Janar Sarki Bello ya maye gurbin Zakari Ibrahim.

A ‘yan watannin baya-bayan nan Najeriya ta yi fama da karuwar munanan hare-hare masu kisa a ciki har da harin kunar bakin waken ranar 26 ga watan agusta a ginin MDD a birnin Abuja. Baicin wadanda su ka rasa rayukan su, akwai kuma wasu mutanen fiye da 80 da su ka ji ciwo a cikin harin.

Wata kungiyar wasu masu tsattsauran ra’ayin addinin Islama mai suna Boko Haram, ta dauki alhakin kai harin. Hukumomin kasar Najeriya sun dorawa Boko Haram laifin tada dimbin boma-bomai da hahharbe wasu mutane har lahira, musamman ma a jahar Borno ta arewa maso gabashin kasar.

XS
SM
MD
LG