Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An rantsar da shugaba Jonathan na Nigeria


People and security forces inspect the site of a car bomb explosion in Basra, southeast of Baghdad, July 29, 2013.
People and security forces inspect the site of a car bomb explosion in Basra, southeast of Baghdad, July 29, 2013.

Lahadin nan aka rantsar da shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan a cikakken wa'adinsa na farko akan ragamar mulki. Duban mutane, ciki harda wasu shugabanin kasashen Afrika ne suka halarci bikin rantsar da shugaban a Abuja, baban birnin taraiyar Nigeria

An rantsar da shugaba Goodluck Jonathan a cikakken wa’adinsa na farko akan mulki. A gaban dubban mutane cikin harda wasu shugabanin kasashen Afrika aka rantsar da shugaban na Nigeria a yau lahadi. Babar kalubalan dake gaban shugaba Jonathan shine yadda zai hada kan kasar, wanda kansu ya rabe bayan tarzomar bayan zaben da suka kashe fiye da mutane dari takwas. In dai ba’a mance ba a watan mayun bara shugaba Jonathan ya dare kan ragamar mulki bayan rasuwar tsohon shugaba Umar Musa Yar’adua. A jawabin daya gabatar bayan an rantsar dashi, shugaba yayi alkawarin inganta harkokin illimi da samar da aiyukan yi da kuma gudanar da harkokin raya kasa a illahirin nahiyar Afrika. Shugaba Jonathan ya kuma ce yana wakilta bege da bukatun dukkan yan Nigeria

XS
SM
MD
LG