Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Red Cross Ta Ce An Kashe Daruruwa A Rikicin Kyrgyzstan


Shugabar rikon-kwarya ta Kyrgyzstan, Rosa Otunabyeva, ta furta talata cewa watakila adadin wadanda aka kashe a biranen Osh da Jalalabad ya zarce 176 da hukumomi suka bayyana.

Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ta bukaci Kyrgyzstan da ta kashe wutar tashin hankalin kabilancin da ya tilastawa mutane fiye da dubu dari biyu tserewa daga gidajensu a kudancin kasar.

Jami’ai sun ce an kashe mutane akalla 176 wasu fiye da 1700 suka ji rauni a hare-haren da ake kaiwa a kan ‘yan kabilar Uzbek a biranen Osh da jalalabad. Jami’an kungiyar agaji ta Red Cross suka ce yawan mutanen da suka mutu ya wuce haka nesa ba kusa ba.

Kungiyoyin agaji sun fara kai kayan agaji zuwa yankunan da abin ya shafa.

Shugabar rikon-kwarya ta Kyrgyzstan, Rosa Otunbayeva, ta fada yau talata cewa duk da wannan tashin hankalin, za a gudanar da kuri’ar raba-gardamar da aka shirya kan sabon tsarin mulki. Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Turai sun roki Kyrgyzstan da kada ta bari wannan tashin hankali ya gurgunta gudanar da wannan kuri’ar raba-gardama da kuma zaben ‘yan majalisar dokokin da za a yi a watan Oktoba.

A halin da ake ciki, ofishin babban kwamishinan kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya yace ya samu shaidar dake nuna cewa wannan tashin hankalin tsara shi aka yi, kuma ya faro ne da wasu hare-hare guda biyar da aka kai lokaci guda cikin daren alhamis a birnin Osh.

XS
SM
MD
LG