Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sauya Wa Ma’aikatan Kiwon Lafiya Wuraren Aiki A Jihar Kano Kan Batun Polio


Rashin aiki kamar yadda ya kamata, da kuma wasu batutuwan gudanar da aiki sun sa an tura sabbin ma’aikatan kiwon lafiya a wasu kananan hukumomin Jihar Kano don karfafa yaki da Polio

Jami’an kiwon lafiya sun bayyana cewa rashin gudanar da aiki kamar yadda ya kamata, da kuma wasu batutuwan da suka sshafi inganin aiki a wasu yankunan kananan hukumomi na Jihar Kano sun sa an sauya ma’aikatan dake bakin dagar yakin da ake yi da cutar Polio.

Ministan kiwon lafiya na Najeriya, Onyebuchi Chukwu, ya fada a lokacin da ya kai ziyara zuwa Hukumar Kiwon Lafiya Matakin Farko ta Kasa a Abuja cewa an gano cewar ayyukan ma’aikatan da aka tura zuwa wasu yankunan kananan hukumomi na Jihar Kano, ba su wadatar kamar yadda aka zata ba.

Yace ainda suke yi yanzu shi ne tura sabbin ma’aikata domin karbar ragamar wannan aikin daga hannun wadanda aka yi imanin cewa bas u tabuka abin kirki.

Yace idan an kwatanta da wasu jihohin kasar nan ma za a ga cewa wasu yankunan kanana hukumomin Kano sun a daga cikin wadanda ke can baya.

Cibiyar Ayyukan Gaggawa Na Kawar Da Polio Ta Kasai ta ma tana da shaidar cewa lallai akwai wasu jami’an gudanar da rigakafi da ake bukatar saukewa daga kan wannan aikin.

Jihar Kano tana daya daga cikin jihohin da har yanzu ake samun bullar cutar shan Inna ta Polio, koda yake yau shekara daya ke nan ba a samun rahton bullar wani jinsin kwayar cutar Polio da ake kira WPV a takaice ba.

Hukumar ta ce duk da wannan, Najeriya tana kan hanyarta ta kawar da cutar Polio, a bayan da ta samu nasarar takaita yaduwar kwayar cutar.

Darektan hukumar kiwon lafiya matakin farko ta Najeriya, Dr. Ado Mohammed, yace a yanzu an takaita inda cutar Polio take zuwa jihohin Borno, Yobe da Kano kawai.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG