Tsamin Dangantaka Tsakanin Ghana Da Burkino Faso Ya Shafi 'Yan Kasuwar Ghana Masu Ratsa Burkino Faso
Dangantaka tsakanin Ghana da Furkino Faso ta yi tsami biyo bayan kalaman shugaba Akufo-Addo a Amurka a bara cewa Burkina Faso ta dauko sojojin haya daga Rasha. Tun bayan nan 'yan kasuwar Ghana da ke dauko albasa daga Nijar sun yi ta fuskantar karuwar hare-hare akan hanyarsu a Burkina Faso.