Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Anya Spain Zata Kai Labari?


An ga kamar 'yan wasan Spain dake rike da kofin gasar wasan kwallon kafa na duniya sun farfado daga kashin da suka sha a wasan su na farko a Brazil, a daidai lokacin da suke ci gaba da karawa yanzu haka da kasar Chile a rukunin su na B.

Idan Spain ta kara shan wani kashi, da kyar ta iya kai labari.

'Yan wasan Netherlands sun kara samun wasu maki uku a yau Laraba bayan sun yiwa Australia ci uku da biyu.

Wasan da za a yi nan gaba a yau Laraba shi ne wanda zai hada Croatia da Kamaru, dukan su 'yan rukunin A, wadanda kuma aka lashe a wasannin su na farko, sannan dukan su biyu su na bukatar samun kyakkyawan sakamako don su ci gaba da jarraba sa'ar su a gasar ta neman cin kofin duniya na wasan kwallon kafa.
XS
SM
MD
LG