Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Atiku Ya Jagoranci Zanga-Zangar Lumana Zuwa Ofishin Hukumar Zabe A Abuja

Tawagar dan takarar jam’iyyar PDP a babban zaben 2023 Atiku Abubakar, ta gudanar da zanga-zangar lumana zuwa hukumar zabe don nuna rashin amincewa da sakamakon zaben.

Zanga-zangar da a ka dade ba a ga irin ta ba, zuwa hukumar Zaben na zuwa ne bayan kotun daukaka kara ta ba da hurumi ga dan takarar na PDP Atiku da na Leba Obi, su duba kayan da a ka yi amfani da su wajen zaben musamman na’urar BVAS da ‘yan adawar su ka ce sam ba a yi amfani da ita ba.

Kakakin kamfen din Atiku, Dino Melaye, ya ce sam ba za su amince da sakamakon ba kuma sun nuna hakan a lokacin da su ka fice daga dakin bayyana sakamakon gabanin kammala kawo sakamakon zaben.

Tawagar ta mika wasika da ke kunshe da dukkan korafe-korafen ‘yan adawar, inda kwamishina mai kula da wayar da kan masu kada kuri’a Festus Okoye, ya karba ya yi alwashin mikawa shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu.


Domin Kari

XS
SM
MD
LG