WASHINGTON, DC —
A Spain, Atletico Madrid tana kan hanyar zamowa zakarar La Liga a karon farko tun 1996. Atletico ta doke Athletic Bilbao da ci 2-1. Lionel Messi ya jefa bugun fenariti a raga, FC Barcelona ta doke Espanyol da ci 1-0, ta ci gaba da zama ta biyu, tana bayan Atletico da maki daya. Real Madrid ta doke Rayo Vallecano da ci 5-0, tana baya da maki 3.
Atletico Madrid na Kan Hanyar Zama Zakarar La Liga - 30/3/14