Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ayi Zaben Don Allah Ba Don Kwadayin Abun Duniya

Shugaban kungiyar Izalatul Bidi'a Wa Iqamatis Sunnah ta Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau
Shugaban kungiyar Izalatul Bidi'a Wa Iqamatis Sunnah ta Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau

Kasa da makoni uku gabanin babban zaben Najeriya, shugaban majalisar Malamai na kasa na kungiyar Jama’atul Izalatul Bidi’a wa’iqamatis sunnah, Sheikh Sani Yahaya Jingir, yayi kira da a tukari zaben cikin lumana.

Yace “Addini Musulunci rayuwa ce gaba daya ciki kuma har da siyasa, yadda ta tunkaro din nan kowa ya tabbatar yaje yayi zaben don Allah ba don kwadayin abun duniya ba kuma ya lura da cancanta ta yanda za’a yi kokarin maido da tsaro a kasar mu da ci gaban bunkasar ilimi, da tattalin arziki, wanda wannan duk bazata yuba sai an lura da cancanta.”

Wakilin mataimakin kasa Barrister Tahir Tahir, ya bukaci yiwa Gwamnati fatar alheri, yana mai cewa “ Gwamnati karkashen shugabancin Goodluck Jonathan, take ta kokari wajen bayarda goyon baya da gudunmawa wajen harkokin ilimi, ta kalli harkar Almajirai, da gina makarantu karo na farko da dai abubuwa da dama da tayi na mutane su ji tsoron Allah sannan kuma su tamaki Gwamnati da adu’a, Allah yasa ayi zaben nan lafiya, kuma Allah yabada nasara da zaman lafiya.”

Kungiyar dai ta gabatar da gidauniyar Naira miliyan dari bakwai da hamsin don gina makarantu da Masallatai a fadi Najeriya, harma da Ghana.

Kungiyar Izala -p 2'48"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00

XS
SM
MD
LG