Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Buri Na A Tsaftace Harkar Fim A Sanya Dokoki - Inji Gidigo


Mika'il Isa bn Hassan
Mika'il Isa bn Hassan

Shirin na Nishadi a Dandalin VOA ya samu bakuncin dan wasa Mika’il Isa bn Hassan, wanda aka fi sani da Gidigo ko Hanci ciki da parlour.

Mika'il ya ce ya samo asalin sunan Gidigo ne shekaru 17 da suka wuce a wani fim, wanda ya ce ya fara fim ne tun yana jami’a a 1994.

Ya ce a wancan lokacin suna harkar fim ne a matsayin drama, inda wata rana ana makon Hausa suna tsaka da wasan ne, sai Dan Magori ya ga yadda yake wasan sa, sai ya neme shi tare da cewar lallai zai kawo sauyi a masana’antar fim.

Hanci ciki da parlour ya ce fim a wancan lokaci, zuwa wannan lokaci, akwai canji mai yawa. A da akwai ladabi da biyayya sabanin yanzu inda masana’antar ba ta da kofar shiga, babu kuma ka’idojin da ya dace.

Babban kalubalen da ya fuskanta a wancan lokacin shine, yadda al'ummar gari ke yi masa kallo, da wasu maganganu da yakan ji daga wajen mutane na zagi, da ire-iren makamantasu.

Ya ce harkar fim ya samu ci gaba masu yawa, domin kuwa fim ya yi masa komai, ciki har da yawon duniya, amma babban burinsa a tsaftace harkar fim, a sanya dokoki da ka’idoji domin inganta masana’antar.

Ga cikakken rahoton daga wakiliyar Dandalin VOA Baraka Bashir.

please wait

No media source currently available

0:00 0:12:22 0:00


Facebook Forum

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG