Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bayern Munich Ta Lashe Bundesliga, 'Yan Man U Kuma Sun Nuna Fusatarsu Kan Tsohon Manaja Sir Alex Ferguson - 26/3/2014

Duk da cewa har yanzu akwai sauran wasanni 6 kafin a kammala wasannin lig-lig na bana a kasar Jamus, kungiyar Bayern Munich ta riga ta zamo zakarar Bundesliga, bayan da ta doke Hertha BSC jiya talata da ci 3-1.

Wannan yana nufin cewa yanzu Bayern tana da maki 77, yayin da ta biyu a teburin lig na Jamus, Borussia Dortmund take can baya da maki 52, watau ratar maki 15. Mutane da dama su na karrama abin tarihin da Bayern Munich ta yi a kan sabon wkach dinta, Pep Guardiola, wanda aka ambata yana fadin cewa kungiyarsa ta nuna karin gwanancewa sosai cikin watanni 10 da suka shige.

A Ingila kuwa, magoya bayan Manchester United ne suka nuna fushinsu a kan tsohon manajansu Sir Alex Ferguson a saboda shi da kansa ya zabi wanda ya gaje shi, David Moyes, wanda bana a karkashinsa, kungiyar ta kasa tabuka komai, tana can matsayi na 7 a wasannin lig-lig na firimiya.

Shi kansa David Moyes bai tsira ba domin kuwa a bayan da Manchester City ta doke su da ci 3-0 jiya talata, wasu daga cikin magoya bayan kungiyar sun fara nuna alamun yin bore.
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:00 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG