Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bom ya Tashe a Kwalejin Ilimi na Gwamnatin Tarayya dake Kano

‘Yan sanda a wurin da bom ya fashe a Kano,
‘Yan sanda a wurin da bom ya fashe a Kano,

Wasu ‘yan bindiga da ba’a san daga inda suke ba sun tarwatsa daliban Kwalejin ilimi, ta gwamnatin tarayya dage Kano, wato FCE a lokacin da suka budewa daliba wuta baya da wani Bom da suka dana ya tashi.

Wasu daga cikindaliban da suka tsallake rijiya da baya sun ce da misalin kafe daya da rabi ne wasu mutane suka zo cikin bakar mota da kuma bakaken kaya suka tada bom sailin na kuma suka farwa mutane da harbe-harbe.

A daidai wannan lokaci kofar makarantar ta kasance a rufe yayin da jami’an agaji ke ci gaba da kai dauki ga wadanda suka raunana, domin yi masu magani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:01 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG