Koch din kungiyar kwallon kafar Arsenal, Arsene Wenger, yace yana da tabbacin cewa dan wasan nan Thierry Henry zai dawo kungiyar Arsenal wata rana.
Arsene Wenger, ya kara da cewa Thierry Henry zai dawo ma kungiyar Arsenal watan watarana, bayan furucin da danwasan yayi na barin kungiyar New York Red Bulls.
Zaman danwasa Henrry a kungiyar Red Bulls tazo karshe ne, bayan rashin nasara a gasar wasan cin kofin MLS Eastern Conference wanda kungiyar New England Revolution ta yi nasara a karshen sati.
Har yanzu dai dan wasan me shekaru 37 bai sanar da matakin shi na gaba ba, amma dan’uwanshi bafaranshe Wenger yace yana da kwarin gwiwar cewa dan wasan zai sake buga wasa a filin wasan daular larabawa.
-
Yusuf Harande
Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.