Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghadafi Ya ce Bai Tsere Nijer Ba Ya Na Libiya Har Yanzu


Moammar Ghadafi ya na kalubalantar masu cewa ya gudu ya gudu ya shiga kasar jamahuriyar Nijer

Moammar Ghadafi ya azalzali rahotannin cewa ya ranci ta kolo daga Libiya ya fada kasar jamahuriyar Nijer

Wani gidan talbijin din kasar Syria ya saka wata muryar da aka ce ta Moammar Ghadafi ce, hambararren shugaban kasar Libiya, ya na azalzalar rahotannin da ke ta baza labarin cewa ya tsere daga kasar Libya ya fada makwafciyar kasar Nijer a cikin wani ayarin motoci.

A cikin furucin da talbijin din Ar-Rai ya yada a yau alhamis, Mr.Ghadafi ya ce rahotanni ne karya da karerayi da aka kitsa da niyyar kashe guiwa, sannan ya nanata cewa har yanzu ya na cikin kasar Libiya. Ya ce magoya bayan shi za su ga bayan kungiyar kawancen tsaron NATO kuma ya ce a shirye su ke su yaki mayakan hukumomin mulkin wucin gadi a Tripoli babban birnin kasar.

Majalisar mulkin wucin gadin kasar ta Libiya ta tura manzanni zuwa kasar jamahuriyar Nijer a wani kokarin neman hana Mr. Ghadafi da mukarraban shi tsallaka kan iyakar kasar don kar su gujewa shari’a. Ba a san inda Ghadafi ya ke ba, kuma gwamnatin kasar jamahuriyar Nijer ta tabbatar da cewa tsohon shugaban kasar Libiyar ba ya kasar ta Nijer.

Jami’an gwamnatin kasar jamahuriyar Nijer sun ce duk abun da su ke yi, sai da sanin majalisar mulkin wucin gadin kuma suka ce motocin da suka shigar kasar Nijer kwanan nan ba su yi yawan da aka bada labari ba.

A halin da ake ciki kuma babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya fada a yau alhamis cewa babu maganar komawa da baya game da matakin canza mulki a kasar Libiya, sannan kumaMDD za ta ci gaba ta taimakawa al’ummar Libiya ta cimma gurorin ta na hakkokin bil Adama da demokradiya.

Babban Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon
Babban Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon

XS
SM
MD
LG