Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Kasar Thailand Ta Umurci Masu Son kansu Da Lafiya Da Su Bar Tungar 'Yan Zanga-Zanga


Hayaki ya turnuke sama a birnin Bangkok, inda 'yan zanga-zanga suek kone tayu a inda suka killace kawunansu.

Gwamnatin ta bayarda wa'adi ga mata da yara da tsoffi da kuma ‘yan zanga-zangar da ba su dauke da makami da su fice daga inda suka yi sansani a yankin kasuwanci na tsakiyar birnin Bangkok.

Gwamnatin Thailand ta bayar da wa’adin nan zuwa karfe 3 na ranar yau litinin agogon kasar, watau karfe 9 na safiyar yau agogon Najeriya, ga mata da yara da tsoffi da kuma ‘yan zanga-zangar da ba su dauke da makami da su fice daga inda suka yi sansani a yankin kasuwanci na tsakiyar birnin Bangkok, babban birnin kasar.

Wani kakakin soja ya fada jiya lahadi cewa dakarun tsaro zasu kyale kungiyoyi ‘yan babu-ruwanmu, kamar kungiyar Red Cross, su shiga cikin yankin da ‘yan zanga-zangar suka yi tunga domin su taimakawa masu son fita.

Hukumomin Thailand sun ce an kashe mutane akalla 36 a fadan da ya barke tun ranar alhamis, ciki har da wani janar na soja da ya bijire ya koma bangaren ‘yan zanga-zangar. A ranar alhamis wani dan kwanton-bauna ya harbi Manjo janar Khattiya Sawasdiphol a kai, kuma a yau litinin ya rasu a sanadin raunin da ya samu. Wasu mutanen su 232 sun ji rauni.

An ji karar harbe-harbe da fashe-fashe har cikin daren nan na lahadi a daidai kofar wasu hotel-hotel na alatu, akasari wadanda suke dab da bakin iyakar inda ‘yan zanga-zangar suka killace suka yi tunga. A wani kasaitaccen hotel mai suna Dusit Thani, an garzaya da bakin dake zaune ciki zuwa wasu dakuna na karkashin kasa domin tabbatar da tsaron lafiyarsu.

A yanzu tayar da kayar bayan da ake yi karkashin jagorancin ‘yan zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati masu suna Masu Jajayen Riguna, ta yadu zuwa wasu sassan birnin na Bangkok, da kuma wasu gundumomin dake lardunan kasar.

Jiya lahadi gwamnatin Thailand ta yi watsi da kiran da Masu Jajayen Riguna suka yi cewar MDD ta zo ta shiga tsakani a tattauna da nufin kawo karshen kwanaki hudun da aka yi ana ba-ta-kashi a Bangkok. Wani kakakin gwamnati, yace ba zasu yarda wata kungiya daga kasar waje ta tsoma baki a harkokin cikin gida na Thailand.

XS
SM
MD
LG