Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Ina Jammiyyar PDP

PDP
PDP

Mataimakin Gwamnan jihar Filato Mr. Ignitius Longjam, ya koka da yadda jama’ar, jihar da dama basu samu katin zabe ba, lamarin da ya bayyana cewa watakila matakin ne na hana wasu gudanar da zabe.

A taron manema labarai da matamakin Gwamnan ya kira ya kuma bayyana cewa bai goyi bayan kiraye-kirayen da wasu keyi na a dage zaben zuwa wani lokaci ba.

Yakara da cewa kada ayi sake a dage zaben domin gudun cewa dage zaben na iya jawo rigima da fatan Allah yasa ayi zaben lafiya.

Dangane da batun zaben fidda gwani kuwa, mataimakin Gwamnan, yace sun rubuta takardan koke ga uwar jamiyyar ta PDP, amma kawo yanzu jamiyyar batace komai ba, ya kara da cewa shi har yanzu ya PDP.

Har yanzu ina PDP - 3'34"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00

XS
SM
MD
LG