Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jama'atu Nasril Islam ta Mike Wajen Yakar Polio


Kungiyar ta tattara masu goyon baya da masu adawa da aikin rigakafin cutar Polio domin musanyar ra'ayi kan wannan aiki a Minna, jihar Neja

Kungiyar Jama'atu Nasril Islam ta mike tsaye domin tabbatar da cewa an kawar da cutar shan inna ta Polio daga Najeriya, kasa kwaya daya tak da ta rage da wannan cuta a duk nahiyar Afirka.

Sakataren kungiyar, Dr. Khalid Aliyu, yace sun tattaro masu goyon baya da wadanda ke yin adawa da aikin rigakafin cutar, suka hallara a Minna Jihar Neja, domin a samar da fahimtar juna, a kawar da irin dari-darin da wasu ke yi.

Cikin wadanda suka halarci wannan taron da kungiyar Jama'atu Nasril Islam ta kira har da karamin ministan kiwon lafiya da wakilan hukumomin kiwon lafiya na kasa da kasa.

Wakilin Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, Mr. Bolaji Buhari, ya bayyana cewa ya zuwa wannan lokaci da ake taron, yara 25 ne aka tabbatar da sun kamu da wannan cuta a jihohi 9 a yankin arewacin Najeriya.

Kwamishinan harkokin ilmi na Jihar Neja, Alhaji Danladi Abdulhamid, ya ce gwamnatin jihar ta lashi takobin cewa in Allah Ya yarda nan da karshen wannan shekara za a daina samun bullar cutar Polio a cikin jihar.

ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari daga Minna.

Jama'atu Nasril Islam Ta Mike Don Yakar Cutar Polio - 2:12
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:12 0:00
Shiga Kai Tsaye

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG