Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaron Israila sun Kashe Wani Ba'amurke dan Asalin Kasar Falasdinu.


Jami'an tsaron Israila sun kashe wani matashi Ba'amurke dan asalin kasar Falasdinu.

Ma'aikatar harakokin wajen Amurka ta yi kira a gaggauta yin bayyanannen binciken gaskiya game da mutuwar Orwah Hammad, dan shekaru 14.

Jami'an tsaron na Israila sun ce wasu suka hana kai hari lokacin da suka bude wuta kan matashin wanda suka ce ya na jefa bom din kwalaba kan wani babban titi da yammacin jiya Jumma'a a garin Silwad a Yammacin Kogin Jordan.

A farkon makon nan, wani Bafalasdine ya tuka motar shi ya afka da ita cikin wata tashar jiragen kasa a birnin Kudus, ya kashe wani dan jaririn wata uku wanda shi ma Ba'amurke ne. Mutane takwas ne suka jikkata a cikin harin na ranar Laraba a tashar jiragen kasan. 'Yan sanda sun harbe matukin motar har lahira.

Tun watan Yunin da ya gabata ake zaman dar-dar a yankin, tun lokacin da mayakan Falasdinawa suka sace matasan Yahudawa uku suka kashe su a Yammacin Kogin Jordan. Daga bisani su ma Yahudawa mayaka suka maida martani suka sace wani Bafalasdine matashi a gabashin birnin Kudus, suka kashe shi, al'amarin da ya ballo tarzomar da ta haifar da yakin kwanaki 50 a Gaza tsakanin Hamas da Israila.

XS
SM
MD
LG