Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karawa Sojoji Karfi Domin ‘Yan Kungiyar Boko Haram

Dr. Mua'zu Babangida Aliyu
Dr. Mua'zu Babangida Aliyu

A yayi da rikicin Boko Haram, yake kara ta’azzara, a yakin arewacin Najeriya, shugabanin yankin na ci gaba da nuna bukatar ganin cewa an karawa Sojoji, karfi da kwarin gwiwa, domin ci gaba da aikin su na yaki da ‘yan kungiyar Boko Haram.

Shugaban Gwamnonin arewacin Najeriya, Dr. Mua’zu Babangida Aliyu, na jihar Neja ne yayi wannan kira a jawabinsa a wurin bukin tunawa da tsofin Sojoji, a garin Minna.

Shugaban kungiyar ‘yan mazan jiya na jihar Neja Abubakar Musa, ya nuna takaicin yadda ‘yan Boko Haram ke fatattakar Sojoji a faggen daga, yace idan aka basu dama suna iya tamakawa da shawarwarin domin cimma nasara.

Mazan jiya Neja - 2'52"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

XS
SM
MD
LG